IQNA

A Yau Ne Ake Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A Saudiyya

23:54 - November 07, 2015
Lambar Labari: 3444466
Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake fara gudanar da gasar karatu da harda da kuma tafsirin kur’ani mai tsarki karo na 37 ta kasarSaudiyya a birnin Makka mai alfarma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bab cewa, wannan gasa an shiryata ne tare da daukar nauyin ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar da kuma cibiyar kula da haramin Makka.

Wannan gasa dai an kasa ta ne zwa bangarori hudu da za a gudanar da ta, da hakan ya hada da bangaren karatu da kum tafsiri gami da tajwidi, sai kuma bangaren hardar dukkanin kur’ani, da kuma bangaren izihi 15, sai kuma bangaren izihi na 5 kamar dai yadda bayanin ya tabbatar.

Dukkanin wadanda suke halartar gasar dai sun fito daga kasashen larabawa da na musulmi da ma wasu wadanda suka zo daga kasashen da ban a musulmi ba, domin raya wannan taro mai matuklar muhimmanci da yake da alaka da kur’ani mai tsarki da kuma addini.

Ahmad bin Ali Sudais, shgaban jami’ar kur’ani a Madina, Nasir bin Saud Al-qithami mataimakin shugaban jami’ar Taif, Khalid bin Ali Muhammad daryani daga jami’ar Algeria, Muhamamd Nasir Sokoto malamin jami’a daga Nigeria, da kuma Abdulkarim Zakariyya harun, daga kasar Mayzia suna daga cikin alkalan wannan gasa.

Daga cikin sharuddan halartar gasar dole ne makaranci ya zama shekarunsa bas u wuce 25 ba, haka nan kuma ya kasance ba fitacce ba ne a kasar da yake.

3444186

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya
captcha