IQNA

Yahudawan sahyuniya Sun Kwace Iko Makewayin Masallacin Alkhali

23:10 - November 08, 2015
Lambar Labari: 3444916
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun kwace iko da wuraren palastinawa da suke gefen masallacin Khalil da hakan ya hada har makewayin masallacin.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, Yusuf Ad’is ministan kula da harkokin addinin na gwamnatin Palastinu ya bayyana cewa, wannan aiki ne na bangaranci, domin masallacin annabi Ibrahim na muuslmi da bas hi da alaka da yahudawa.

Wasu rahtanni sun ce wasu gungun manyan malaman Yahudawan Sahayoniyya sun bukaci tsagerun Yahudawa ‘yan kaka gida da su aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar Palasdinu.

Jaridar Haramtacciyar kasar Isra’ila ta yadiut a bugunta na yau Asabar ta habarta cewa; Manyan malaman Yahudawan Sahayoniyya ashirin da tara sun fitar da bayanin hadin gwiwa kan kira ga tsagerun Yahudawa ‘yan kaka gida da su dauki matakin aiwatar da kisan gilla kan duk wani bapalasdine.



Sasannan bayanin ya jaddada yin kira ga mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan su dauki mataki mai gauni kan batun Palasdinawa.



Kimanin palastinawa dubu 200 ke zaune a madinatul Khalil, wannan kira na manyan malaman Yahudawan Sahayoniyya ya zo ne a daidai lokacin da tsagerun Yahudawan Sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke samun kariyar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai farmaki kan gidajen Palasdinawa a yankunan da suke garin Khalil a gabar yammacin kogin jodan.



Tsohon shugaban Isra’ila ya mutu



Ishaq Naun tsohon shugaban haratacciyar kasar Isra’ila yam utu yana da shekaru 94 da hahiwa  a duniya, ya karbi mukamin ne tun shekarar 1978 har zuw 1983, ya kasane a gaba wajen kula yarjejeniyar sulhu a Masar a lokacin mulkin Anwar Sadat na kasar ta Masar.

3444694

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha