Kamfanin dillancin labaran iqna ya hbarta cewa ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a ministan kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa an gina masallatai fiye da 1000 a fadin kasar a cikin shekara daya duk kuwa da cewa an ware kafin kudin gina masallatai 779 ne baki daya.
Ya ci gaba da cewa kasar Masar ta yi suna aduniya wajen gina masallatai a dukkanin birane da kauyuka domin amfanin muslumi, saboda anan ne ake gudamnar da ayyuka na ibada, da hakan ya hada da salloli da kuma wasu taruka na addini.
Al’ummar kasar Masar na baiwa masallaci matukar muhimamnci bisa ga al’ada da mutaen kasar suke da ita atarihinsu na muslunci, kuma hakan ya zama wata alada wadda ta ci gaba har wannan zamani.
Ya kara da cewa za su yi iyakacin kokarinsu domin sanya ido kan dukaknin ayyukan da suke gudana amasallatai, domin kada hakan ya zama wani wuri na yana munan akidu na ta’addanci da wanke kwakwalen matasa.
Kamar yadda kuma ya ce wajibi ne kan malami da su yi amfani da wannan damar domin yi matasa saiti kan hakikanin koyrwar addini, ba irin ta masu kafirta al’ummar musulmi ba.