IQNA

Taron Ministocin Harkokin Addini Da Masu Bayar da Fatawa Na Kasashe 70 A Masar

22:35 - November 14, 2015
Lambar Labari: 3449516
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani taro wanda shi ne karo na ashirin da biyar da na ministocin harkokin addini da masu bayar da fatawa na kasashen musulmi a birn Al-akasar na kasar Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alahram cewa, daga yau ne ake gudanar da wani taro wanda shi ne karo na ashirin da biyar da na ministocin harkokin addini da masu bayar da fatawa na kasashen musulmi 70 a birn Al-akasar na kasar kamar yadda rahoton ya nuna.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron dai za a bude shi karkashin jagorancin shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi, da kuma shugaban cibiyar Azahar Ahmad Tayyib, da kuma Muhammad Kukhtar Juma’a ministan mai kla da harkokin addini na kasar.

Ministan addini na Palastine, Mai bayar da fatawa a Quds, masu byar da fatawa na Chadi, Ukraine, shugaban cibiyar Ibn Sina Paris, shugaban Bait Zakat Kuwait a Kahira,ministan addinina Srilanka, ministan addinai India, shugaban musulmin Japan, mai bayar da fatawa a Australia, wasu daga cikin jakadn kasashen larabawa da na musulmi na daga cikin mahalarta taron.

3447897

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha