IQNA

Za A Gudanar Da Taron karawa Juna Sani Kan Ilmomin Kur’ani A Madina

19:55 - November 17, 2015
Lambar Labari: 3453887
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taron karawa juna sani mai taken mudala’ar kur’ni mai tsarki a birnin Madina mai alfarma.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na  tafsir.net cewa, a yau ne shirin da ake kira na Sarki Abdulaziz za a gudanar da wani zaman taron karawa juna sani a jami’ar mai taken mudala’ar kur’ni mai tsarki a birnin na Madina.

Hekmar Bashir daya daga cikin malamai masu kula da koyar da ilmomin kur’ani mai tsarkia  jami’ar ta Madina shi ne zai gabatar da jawabi a yau.

An jima dai ana gudanar da wannan shiri na Malik Abdulaziz a kasar musamamn a jami’oi inda ake yin bahasi da kuma karawa juna sani kan lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki da kuma tafsirinsa, tare da halartar malamai na jamioi da kuma dalibai a wanann bangare.

Babbar manufar gudanar da wannan taron dai ita ce kara karfafa masu bincike kan lamurra da suka danganci wannan kwas na ilmomin kur’ani mai tsarki, yanzu haka dai akwai malamai da za su gabatar da jawabi a bangarori daban-daban na taron.

3453172

Abubuwan Da Ya Shafa: madina
captcha