IQNA

Wani Dalibin jami’a A Palastinu Ya Hardace Kur’ani A Cikin Kwanaki 17

23:00 - November 21, 2015
Lambar Labari: 3455354
Bangaren kasa da kasa, Subh Wajih Alqaiq dalibin jami’a ne a yankin zirin Gaza palastinu da ya hardace kur’ani mai tsarkia cikin kwanaki 17.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar giz na Palastinu online cewa, wanann dalibin jami’a shi ne mutum na farko a yankin Zirin gaza da ya hardace kur’ani mai tsarki a cikin kankanen lokaci haka.

Sobh Wajih Alqaiq ya ce ya samu wannan damar ne ta hardace kur’ani mai a cikin wannan kankanuwar mudda tare da taimakon Allah madaukakin sarki, wanda yaba shi wannan damar.

Ya ci gaba da cewa ya yi tsari ne domin cimma wannan buri, inda ya samu damar hardace kur’ani mai tsarkia  cikin kasa da kwanaki 30, wanda hakan ya zama wata babbar nima ta ubangiji a gare shi.

Sobh dalibi ne na jami’a wanda yake karu a bangaren physics kuma yana karatun a bangaren digiri na uku ne, inda ya ce zai rubuta littafai 12 bayan kammala karatunsa.

Ya rubuta wani littafi kan ilimin taurari a lokacin da ya shiga jami’ar Aqsa kuma yanzu haka masu bincike suna duba littafin nasa.

Wannan dalili ya samu yabo daga masa da dama da suka duba irin abubuwan da ya yi rubutua  kansu inda suka sheda iliminsa.

3454891

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha