IQNA

Kona Kur’ani Da Da Masallatai Shhi Ma Aiki Ne Na Ta’addanci

23:29 - November 22, 2015
Lambar Labari: 3455814
Bangaren kasa da kasa, Ali Al-nu’aimi ya bayyana cewa; kone kwafin kur’animai tsarki da masallatai da ake a kasashen turai shi kansa wani naui na ta’addanci.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawwaba News cewa, Ali Al-nua’imi shugaban kwamitin musulmi mai kula da lamurran turai a karkashin jagorancin Ahmad Tayyib sheikuhl Azhar ya yi kakausar suka kana bin da ke faruwa kan musulmi a turai.

Inda y ace ko shakka babu kone kwafin kur’animai tsarki da kuma kona masallatai da ake yi a cikin kasashen turai shi kansa wani naui ne na ta’addanci a kan bil adama.

Dangane da abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi kan palastinawa kuwa, ya bayyana cewa shi ma take hakkokin bil adama ne wanda babu wani dalili ko wata huja da za a iya kare hakan.

Ali Al-nu’aimi a bangaren hare-haren da aka kai kasar Faransa kuwa, ya bayyana cewa suna yin Allawadai da kakausar murya kan hakan, tare da tabbatar da cewa ta’addanci bas hi da wata alaka ko dangantaka da addinin muslnci.

Sai kuma daga karshe ya kirayi malamai da masana addini da su yi iyakacin kokarinsu domin bayyana wa mutane cewa akwai banbanci a tsakanin masu kiran kansu musulmi suna aikata ta’addanci da kuma musulmi na gaskiya.

3455543

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha