IQNA

Babban Mai Bayar Da Fatawa A Dubai Ya Halasta Buga Kwafin Kur’ani Mai Launi

23:31 - November 22, 2015
Lambar Labari: 3455815
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Abdulaziz Alhaddad ya bayyana cewa ya halasta a buga tare da karanta kur’ani mai rsaki mai launi kamar yadda aka yi a kasar Masar.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ae24 cewa, Ahmad Abdulaziz Alhaddad babban mai bayar da fatawa kuma daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a Dubai ya bayyana cewa ya halasta a buga tare da karanta kur’ani mai rsaki mai launi.

Ahmad Abdulaziz Alhaddad ya ci gaba da cewa babu wani dalili na harmta karanta irin wadannan kur’anai da aka buga da rubuta mai kala.

Alhadda y ace buga kur’ani a cikin launi mai kala halas ne matukar dai za a buga shi a kan rubutun Usman Taha.

Ya kara da cewa yin amfani da kaloli ma yak an taimaka ma malamai masu koyar da kur’ani mai tsarki, domin kuwa rubutun ya zama mai kala to za a iya bambance kaidoji na tajwidin kur’ani mai tsarki cikin sauki ga dalibai da suke koyo.

Alhadda ya ci gaba da cewa ana iya yin amfani da kalollin rubutun ma wajen bayyana manonin ayoyi, inda ake aka samu aya tana Magana kan rahma da tausayi sai a yi amfani da kala da ta dace da hakan, dangane da azaba ma ana iya yin amfani da kala daidai da abin ake Magana a kansa.

3455558

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha