IQNA

Jami’an Tsaron Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Farmaki A Wani Masallaci

23:14 - November 28, 2015
Lambar Labari: 3457979
Bangaren kasa da kasa, a yau da safe jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wani farmaki a kan wani masallaci a cikin birnin Alkhalil da ke gabar yamma da kogin jodan.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Petra na kasar Jordan cewa, da asubahin yau  jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wani farmaki a kan wani masallaci a cikin birnin Alkhalil inda suka lakada wa masallata duka.

Bayanin ya ce sojojin yahudawan Isra’ila sun harbe wani matashi bapalastine a yau Alhamis a gabacin birnin a lokacin da daruruwan jami’an sojin na Isra’ila suka kutsa kai a yankina yau suna farautar Palastinawa.

Mai aiko ma tashar talabijin ta Alalam rahotanni daga gabacin birnin ya bayyana cewa, jami’an sojin na yahudawan Isra’ila sun harbe matashin mai suna Yahya Yusri Taha ne a yau da harsashin bindiga, inda a nan take ya yi shahada.

A jiya ma sojojin an Isra’ila sun kashe wasu matasa palastinawa biyu da sekarunsu ba su zuwa 17 a garin Madinatul Khalil da ke gabar yamma da kogin Jordan, wadanda su ma suka yi shahada.

Ma’aikatar kiwon lafiya a Palastinu ta sheda cewa daga farkon watan ktoban da ya gabata ya zuwa yanzu, palastinawa dari daya ne suka yi shahada, 18 daga yankin zirin Gaza, daga cikinsu kuwa akwai kakanan yara ashirin da biyu, da mata hudu.

3457831

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha