IQNA

Za A Fara Koyar Da Tajwidi Da Kuma Hardar Kur’ani A Makarantun Masar

23:26 - December 01, 2015
Lambar Labari: 3459309
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar ilimi ta kasar Masar ta bayyana cewa za a fara koyar da ilimin tajwidi da kuma hardar kur’ani mai tsarkia makarantun kasar Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Eram cewa, Al-sharbini Alhilali mitar ma’aikatar ilimi ta kasar Masar ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara koyar da ilimin tajwidi da kuma hardar kur’ani mai tsarkia  makarantun kasar baki daya.

Ta ce babbar manufar hakan ita ce samar da wani yanayi na fahimtar manufofin addinai a kasar musamman addinin muslunci da kiristanci, wadanda su ne manyan addinai na kasar.

Dangane da yadda za a fara aiwatar da shirin kuwa minister ta bayyana cewa dalibai za su gudanar da hardar kur’ani da kuma koyar da su ilimin tajwidinsa domin sanin yadda ake karatun kur’ani da kuma fahimtar ma’anoninsa.

Bayan hakakuma za a rika gudanar da gasar hardar kur’ania  tsakanin daliban makarantu na kasar ta Masar baki daya, domin ta haka ne za a kara samun damar fahimtar da yara koyarwar kur’ani ta gaskiya, domin kauce wa fadawarsu a kan tafarkin da ke rusa akidar matasa musulmi suna shiga ayyukan da bas u da alaka da musulmi da suna suna addini.

Alhilali ta ce yanzu haka ta bayar da umarnin fara aiwatar da wannan shiri a dkknin makarantu na firamare da sakandare na kasar baki daya, wanda kuma tuni aka fara gudanar shirin yin haka a dukaknin makarantu, kuma hakan ya samu karbuwa daga al’ummar kasar wadanda akasarinsu dama mabiya muslunci ne.

3459112

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha