IQNA

Ziyarar Arbaeen Tana Da Muhimmanci Wajen Hada Kan Musulmi

23:40 - December 03, 2015
Lambar Labari: 3459635
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa ga Ahlu Sunna a Iraki Sheikh Mahdi Alsumaidai ya bayyana ziyarar arbaeen a matsayin wani lamari mai muhimamnci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Furat News cewa, Sheikh Mahdi Alsumaidai babban malami mai fatawa na Ahlu suna airaki ya cwa, ko sakka babu wannan tari na arbaeen yana da muhimmanci wajen hada dukkanin al’ummar musulmi.

Babban malamin ya kara da cewa, wannan taro an saba gudanar da shit un tsawon shekaru a kasar Iraki, kuma dukaknin bangarori na musulmin Iraki suna halarta, domin kuwa Imam Hussain (AS) na dukkanin musulmi ne baki daya.

Ya ce ko shakka bayar da muhimamnci ga wannan tarao yana da alfanu matuka ga dukaknin al’ummar musulmi, domin kuwa lamari na addini wanda ya hada musulmi daga kasahen duniya, wanad suke da fahimta daban-daban, amma sun hadu kan son iyalan gidan manzo.

A kan hakan ya yi kira da a kara daukar matakan da suka dace kara fada wannan lamari da kuma tsara shi, ta yadda dukaknin musulmi za su samun hadin kai da fahimtar juna a labarkacin wadannan taruka masu albarka.

Tun daga farkon watan safar ne dai musulmi daga koina cikin Iraki da keawaye suka fara tattaki zuwa Karbala domin halartar tarukan arbaeen.

3459372

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha