Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wafd cewa, , Abbas Shoman a lokacin da yake gabatar da wani jawabi ya yi kira ga kafofin yada labarai na kasashen muuslmi da na larabawa da su kare fuskar muslunci a duniya sakamaon ayyukan ta’addanci da ake aikatawa da sunan addinin muslunci.
Jami'ar ta kasar masar ta bayyana damuwarta dangane da yadda 'yan kungiyar ta'addancin nan ta daesh suke amfani da kananan yara wajen aikata ta'addanci da kuma ayyukan leken asiri.
A cikin wani rahoto da Cibiyar bincike ta rasad da ke da alaka da jami'ar ta Al-Azhar ta fitar ta bayyana cewar ya zuwa yanzu kungiyar daesh din ta sami nasarar janyo dubban matasa daga kasashe daban-daban na Yammaci zuwa cikin kungiyar don cimma manufofinsu na ta'addanci.
Rahoton ya kara da cewa 'yan kungiyar ta suna amfani da irin rashin masaniyar da wadannan matasan suke da ita na koyarwar addinin Musulunci wajen sanya su aikata ayyukan ta'addanci da sunan Musulunci.
Har ila yau cibiyar ta jiyo wasu daga cikin kananan yara 'yan shekaru biyar zuwa sha biyar da suka gudu daga kungiyar suna fadin cewa tsawon lokacin zamansu tare da 'yan kungiyar an koyar da su nau'oi daban-daban na ayyukan ta'addanci da suka hada da yanke kawukan mutane da sauran.