Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Guardian cewa, Mahmud saleh daya daga cikin matafiyan yana cewa, duk da cewa akwai yiyiwa mayakan na alshabab su halakasu gaba daya musulman sun ki ware wa har sai yan ta’addan suke tafi.
Musulmai a wani hatsarin da ya auka masu a arewacin Kenya sun taimaki kiritocin da suke tare da don su tsira da ransu. Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto wani musulmi wamda yake cikin mutanen da mayakan kungiyar alshaban goma sufa tsaida motar bus da suke cikinta a wani wuri a arewacin kasar ta Kenya.
Inda yace suka bukaci musulmi su ware daga kiritoci ammam suka ki yin haka, sannan wasunsu ma suka bawa kiristocin da suke tafiya tare wasu kayakinsu kamar dan kwali da dogayen riguna don su boye Kaman ninsu.
Duk da cewa akwai yiyiwa mayakan na alshabab su halakasu gaba daya musulman sun ki ware wa har sai yan ta’addan suke tafi.
A cikin shekara ta 2011 Kenya ta fusknci a irin wadannan matsaloli na tsaro daga yan ta’addan Shabab na kasar Somalia.
Haka nan kuma kwanakin baya ma yan ta’addan sun kashe mabiya addinin kirista 28 a cikin motar bus a wani yanki na kasar.