IQNA

20:25 - February 06, 2016
Lambar Labari: 3480115
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin manyan malaman addinin muslunci yan sunna daga kasar Lebanon sun taya al’ummar Syria murna dangane da kwace iko da yankuna daga hannun yan ta’adda na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ha barta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aran News cewa, Sheikh Suhaib Alhalabi malamin addinin muslunci a kasar Lebanon daga mabiya tafarkin sunna, ya nuna farin ciki matuka kan fatattar yan ta’adda a Syria.

Ya bayyana nasarar da sojojin kasar ta Syria tare da kawayensu suka samu a matsayin wani bababn abin alfahari ga dukaknin al’ummomin kasashen Syria da Lebanon da ma sauran kasashe masu yanci, wadanda suke fada da hankoron yan mamamya da kuma ‘yan ta’adda.

Shi ma a nasa bangaren Sheikh Ahmad Qattan daya daga cikin malaman ahlu sunna akasar ta Lebanon ya bayyana cewa, abin da ya faru abin sa albarka ne, tare da yin fatan a samu irin wanann nasara asauran yankunan da suke hannun yan ta’adda a yanzu.

Ya ce bababr fatar da ake da ita ce dukaknin yankunan kasar Syria su samu yanci daga mamamyr yan ta’adda, domin idan Syria ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, hakan babban kalu bale ne ga Isra’ila da Amurka.

3473187

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: