IQNA

23:36 - February 22, 2016
Lambar Labari: 3480163
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib babban malamin jami’ar Azahar ya bayyan acewa shia da sunna bangarori ne guda biyu da ske a matsayin fukafuki ga addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al’umma Ikhbariyyah cewa, Ahmad Tayyib a lokacin da yake ganawa da malaman Azahar a kasar Indonesia ya bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya a fitar da shi’a daga addinin muslunci.

Y ace ya zama wajibi a kawo karshen tatsauran ra’ayi da wuce gona da iri a cikin addini, domin hakan shi ne ke kai msuulmi zuwa ga rudani da kafirta juna, wanda kuma ba koyarwar5 addinin muslunci ba ne, babu wanda zai iya fitar da musulmi shia daga muslunci.

Shekhul Azahar ya kara da cewa, shi’a da sunna bangarori ne guda biyu na addinin muslunci da suke a matsayin fukafukinsa da ske dauke da shi.

Daga karshe ya kirayi masu tsatsauran ra’ayin da ta’assubanci akida da su guji fitar da shi’a daga muslunci, domin hakan yana tattare da babban hadari.

3477613

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: