IQNA

Netanyahu Ya Jinjina Wa Matakin Larabawa Yankin Tekun Fasha

20:36 - March 08, 2016
Lambar Labari: 3480214
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan haratacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jinjinawa larabawan yankin tekun fasha dangane da saka kungiyar Hizbullah a cikin yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, ya nakalto daga jaridar Alakhabar ta kasar Lebanon cewa, Benjamin Netanyahu ya jinjinawa larabawan yankin tekun fasha dangane da saka kungiyar Hizbullah a cikin yan ta’adda tare da bayyana hakan a matsayin aiki mai kyau.

Netanyahu ya bayyana hakan nea zaman da majalisar dokokin Isra’ila ta gudanar, inda yake cewa shin kungiyar Hizbullaha halin yanzu za ta iya cewa sub a yan ta’adda ba ne? alhali kuwa sarakunan larabawa da kansu sun kira su yan ta’adda, ya ce yana jiran amsa daga jagororin wanann kungiya.

Ya ci gaba da cewa hakika wannan mataki da kasshen larabawan yankin tekun fasha suka dauka zai kara taimaka ma alakar da ke a tsakaninsu, domin kuwa suna makiyi guda ne shi ne Hizbullah da kuma da kuma masu daukar nauyin wanann kungiya.

Larabawan yankin tekun fasha dai a zaman taron da suka gudanar a cikin makon da ya gabata, sun bayyana kungiyar Hizbullah mai gwagwarmayar musulunci a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Da dama daga cikin masu bin diddigin abin da yake faruwa dai sun bayyana wanann mataki a matsayin aiwatar da wani umarni kawai da aka baiwa wadannan sarakuna, wadanda ba za su iya aiwatar da wani abu ba sai abin da aka umarce.

3481795

captcha