IQNA

Kotun Duniya Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 40 A Kan Makashin Bosniyawa

23:56 - March 25, 2016
Lambar Labari: 3480263
Bangaren kasa da kasa, kotun duniya mai shari'ar manyan laifukan yaki ta yanke wa tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic hukunci daurin shekaru 40 a gidan yari.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga Euro News cewa, yayin da yake sanar da hukumci, babban alkalin kotun Alkalan kotun mai shari'a ya ce alkalan kotun sun sami Radovan Karadzic da hannu cikin laifuffuka goma cikin laifuffuka sha daya da aka zarge shi da shi a gaban kotun da suka hada da kisan kiyashi tare da tilastawa al’umma barin gidajensu don haka kotun ta daure shi shekaru 40 a gidan zama.

Har ila yau kotun ta sami Mr. Karadzic dan shekaru sabain a duniya da hannu cikin kawanyar da aka yi wa garin Sarajevo daga watan Mayun zuwa Oktoban 1995 lamarin da share fagen kashe dubban mutanen garin.

Radovan Karadzic dai shi ne ya jagoranci sojojin Sabiya a kisan kiyashin da suka yi wa musulmi a yankin Srebrenica da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1995, inda suka kashe musulmin yankin kimanin dubu takwas baya ga wasu dubban kuma da aka kashe a yayin yakin na Bosniya wanda aka bayyana shi da cewa shi ne ta'asa mafi muni da aka aikata a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

3484471/40

captcha