IQNA

17:37 - March 31, 2016
Lambar Labari: 3480280
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya sun hana mabiya mazhabar shi’a ayankin Ihsa yin kiran sallah.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, ya nakalto shafin Alhad cewa mahukuntan wahabiyan Saudiyya sun kafa dokar hana kiran salla a masallacin mabiya mazhabar shi’a acikin lardin na Ihsa.

Baya kama Ayatollah Hussain Radi sun kafa wasu dokoki masu tsauri, daga ciki kuwa har da takaita hudubar juma’a da kuma hana bude masallatai a ranar Juma’a sai karfe sha biyu da rabi na rana.

Wadannan dai na daga cikin irin matakan da mahukuna wahabiyawan na Saudiyya suke dauka domin takura yan shi’a da hana su gudanar da lamurransu kamar yadda suka fahimta, tare da tilasta su bin abin da wahabiya suke gani.

Tun bayan da aka fara gudanar da jerin gwano na kin amincewa da salon mlkin mulkin mulukiya akasar a cikin shekara ta 2011, mahukuntan wahabiyawan na Saudiyya suka fara daukar matakai na rashin imani fiyec da wanda suke dauka a lokutan baya.

3485002

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: