IQNA

Haramcin Zubar Da Jinin Dan Adam A Addinin Muslunci A Jordan

22:26 - April 10, 2016
Lambar Labari: 3480311
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro mai taken haramcin zubar da jinin dan adama a mahangar addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na egynews.net cewa, a jiya ne aka gudanar da wani zaman taro a kasar Jordan mai taken haramcin zubar da jinin dan adama a mahangar addinin musulunci da kuma yadda muslunci yake girmama mutum.

Nuhammad Habash Alalam daya ne daga cikin masana na kasar Syria wanda ya halarci taron, kuma ya bayyana cewa hakika abin da yake faruwa dangane da ta’addanci a halin yanzu ya samo asali ne daga rashin fahimtar hakikanin koyawar addinin muslunci ta zaman lafiya.

Muhamamd Alahmari shi ma ya wani daya ne daga cikin masu halratr wannan taro, wanda shi me ya bayyana cewa, wasu suna ta kokarin su fitar da wata mumunar sura da hauka da dabbanci dangane da muslunci ta hanyar ayyukansu, kuma musulunci ya barranta daga gare su.

Abdul Mahmud Abu daga kasar Sudan, wanda kuma shi ne shugaban reshen kungiyara wannan kasa, shi ma ya gabatar da nasa jawabi kan muhimamncin zaman lafiya a mahangar addininmuslunci.

Abin tuni a na dais hi ne, wannan kungiya tana rassa daban-daban a kasashen duniya, da hakan ya hada da kasashen Sudan, Moroccow, Aljeriya, Mauritaniya, Tunisia, Iraki, Pakistan da kuma kasar Yemen.

3487168

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha