IQNA

An Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Jagoran Jam’at Islami A Bangaladesh

21:04 - May 11, 2016
Lambar Labari: 3480402
Bangaren kasa da kasa, an zartar da hukuncin kisa kan jagoran kungiyar Jama’ar Islami Miti Rahman Nizami a kasar Bangaladesh.
Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Aljazeera cewa, rahotanni daga kasar Bangalesh sun bayyana cewar an zartar da hukuncin kisa da aka yanke wa jagoran jam'iyyar Musulunci mafi girma a kasar.

An yanke hukncin ne bisa laifin da aka same shi ya aikata a lokacin yakin fafutukan neman 'yancin kasar daga Pakistan a 1971.

Rahotannin sun jiyo ministan shari'a na kasar Anisul Huq, yana fadin cewa an rataye Motiur Rahman Nizami, shugaban jam'iyyar Jamaat-e-Islami dan shekaru 73 a duniya a babban gidan yarin Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh din ne a daren jiya, mako guda bayan kotun koli ta yi watsi da wani roko na karshe da ya gabatar na a sake duba hukuncin kisar da aka yanke masa.

Masu shigar da karar dai sun bayyana cewa Motiur Rahman Nizami shi ne ya kafa kungiyar al-Badr ta masu dauke da makami wadanda kuma suke goyon bayan kasar Pakistan a shekarar 1971, da ake zargi da kashe mutane da dama da suka hada da marubuta, likitoci da 'yan jarida da sauran al'ummar kasar a lokacin yakin da Bangaladesh ta yi na neman 'yan cin kai daga Pakistan.

Nizami shi ne mutum na na hudu cikin jerin shugabanin jam'iyyar ta Jamaat-e-Islami da aka aiwatar da hukuncin kisa a kan su tun bayan da firayi ministan kasar Sheikh Hasina ta kafa kotun shari'ar laifuffukan yaki a kasar a shekara ta dubu biyu da tara.

3496957

captcha