IQNA

Mutane 3 sun kwanta Dama Sanadin Harin Ta'addanci A Masallaci A Tanzania

22:38 - May 21, 2016
Lambar Labari: 3480435
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai kan wani masallaci a yankin Muwanza da ke yamma maso kudancin Tanzania mutane uku da suka hada da limamnin masallacin sun rasu.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar International business times cewa, akalla mutane uku ne su ka kwanta dama sanadiyyar harin ta'addanci da aka kai a masallacin garin Mowanza da ke arewa maso yammacin kasar Tanzania.

A yau asabar ne Cibiyar watsa labaru ta International Business Timer ta ambaci cewa an kai harin ne a masallcin na Rahmani, tare da kashe mutane 3 da su ka hada da limamin masallacin.

Majiyar ta ci gaba da cewa; mutane 15 ne su ka kai harin suna rufe da fusakunku, inda su ka bude wute akan masallata.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin, sai dai ana zargin kungiyar Da'esh, ( Isis) da hannu.

3499751

captcha