IQNA

An kawo Karshen Gasar Kur'ani ta Kasar Jibouti

23:45 - June 23, 2016
Lambar Labari: 3480543
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Jibouti a jiya.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, an kawo karshen gasar ne tare da halartar manyan jami'ai inda aka bayar da kyautar shugaban kasar ga wadanda suka nuna kwazo daga cikin wakilan kasashe 10 da suka halarci gasar.

Kasashen kuwa sun hada da Somalia, Yemen, Sudan Kenya, Algeriya, Uganda, Ethiopia Komoros da ita kanta Jibouti, haka nan kuma babbar cibiyar kula da ayyukan addini ta kasar ita ce ta dauki nauyin shiya wannan gasa.

A bangaren harda da karatun kur'ani da salon a tartili da kuma tajwidi wakilan kasashen Sudan da kuma Kenya suka a mataki na farko.

Abdulkadir Kamil Muhammad Firayi ministan kasar Jibouti ya bayyana a wurin taron rufe gasar cewa, ko shakka babu gudanar da irin wadannan taruka na kur'ani yana da matukar muhimamnci a kasar, domin kuwa yana raya ruhin jama'a.

Ya kara da cewa, baya ga haka gudanar da gasar a cikin wannan wata mai alfarma yan ada matsayi na musamman, domin kywa awannan lokaci dukkanin al'umma musulmi take komawa ga kur'ani ta hanyar karatu da wa'azi da tafsirinsa.

Mu'min Hassan Birri ministan al'au na kasar shi ma ya taya dukaknin wadanda suka halarci gasar murnar samun wannan dama da kuma yin kira da a kara bayar da himma kan hakan.

Tuna cikin shekara ta 1999 ne dai aka fara gudanar da wannan gasa da shugaban kasar Isma'ila Umar Gili yake bayar da kyauta.

Kasar Jibouti dai kasa karama matuka a cikin nahiyar mai mutane dubu 400 kacal.

3509524

captcha