Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa a yammacin yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wasu gungun iyalan shahidai ciki har da iyalan shahidan ranar 7 ga watan Tir (wato Ayatullah Beheshti da abokan aikinsa) da iyalan shahidai masu ba da kariya ga haramin Imaman Ahlulbaiti (a.s) daga hare-haren ‘yan ta'addan Da'esh inda yayin da yake jinjinawa irin "imani, kokari da gagarumar fahimtar da shahidan suke da ita, bugu da kari kan hakuri da tsayin dakan iyalan shahidai masu girman, ya bayyana su a matsayin tushen tsayin daka da karfin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Daga nan sai ya ce: Hanya guda kawai ta tabbatar da ci gaban Iran, ita ce raya ruhin juyin juya hali da kokari da tsayin daka.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da isar da sakon juyayin shahadar Imam Amirul Muminin Ali (a.s) inda ya bayyana Imam Ali (a.s) a matsayin babban shahidin tarihin bil'adama, kana kuma shahidin masallaci da tafarkin gaskiya da tsayin daka. Haka nan kuma yayin da yake ishara da gushewar shekaru 35 da faruwar harin ta'addancin da aka kai wa helkwatar jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci a ranar 7 ga watan Tir shekarar 1360 (28 Yunin 1981 - da yayi sanadiyyar shahadar Ayatullah Beheshti da abokan aikinsa), Jagoran ya bayyana cewa: Shekara da shekaru kenan ‘yan ta'adda marasa imani da suka kai wannan harin, bayan sun gudu daga kasar nan suke karkashin kulawar kasashen Turai da Amurka da suke da'awar jagorancin fada da ta'addanci da kuma kare hakkokin bil'adama.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wannan lamarin a matsayin babban abin kunya na tarihi a wuyan kasashen Turai da Amurkan yana mai cewa: Wadannan ‘yan ta'addan mutane ne wadanda sun shigo tafarkin gwagwarmaya ne bisa ikirarin kare bil'adama da kuma Musulunci, to amma daga baya sun aikata munanan ayyuka da suka hada da harin ranar 7 ga watan Tir (28, Yuni, 1981) da zubar da jinin mutane fararen hula da ba su ci ba su sha ba, daga karshe kuma suka zamanto tare da mutane irin su Saddam, a halin yanzu kuma suna karkashin inuwar kariyar Amurka.
Ayatullah Khamenei ya bayyana harin 7 ga watan Tir na shekarar 1360 (hijira shamsiyya) a matsayin wani lamari mai girma da ke dauke da darussa masu yawa. Haka nan kuma yayin da yake bayyana rashin jin dadinsa kan gazawar da aka nuna wajen bayaninn lamurra masu muhimmanci da suka shafi juyin juya halin Musulunci da shahidai zuwa ga matasa da zuriya masu zuwa, Jagoran ya bayyana cewar: Bayan gushewar shekaru 35 amma har ya zuwa yanzu ba a shirya wani fim na sinima ko kuma wata drama ko kuma wani littafi dangane da harin 7 ga watan Tir din da Shahid Beheshti da sauran shahidan wannan harin ba. Ruhin juyin juya halin da ke tattare da mutane ne ya ci gaba da rayar da wannan lamari.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan littafan da aka rubuta da suke da alaka da hare-haren soji da aka kai yayin kallafaffen yaki da kuma shahidan kallafaffen yaki, Jagoran ya kirayi dukkanin al'umma musamman matasa zuwa ga karanta irin wadannan littafa yana mai cewa: Duk da cewa akwai an rubuta littafa da dama kan wannan batu, to amma har ya zuwa yanzu akwai fagen ci gaba da rubuta wasu littafan kan bangarori daban-daban na kallafaffen yaki da kuma shahidansa masu girman matsayi. Don kuwa halaye, maganganu da kuma yanayin yunkurin kowane guda daga cikin shahidan, wani fage ne mai fadin gaske.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa daya daga cikin siffofi na musamman da lokacin kallafaffen yaki ya kebanta da shi, shi ne kasantuwa da shigowa fagen dukkanin bangarori daban-daban na al'umma cikin shauki da kumaji ba su bar lamarin kawai ga sojojin gwamnati ba. Don haka sai ya ce: A yau nasihar da nake yi wa jami'an gwamnati ita ce cewa su yi kokarin amfanuwa da karfi irin na mutane a dukkanin bangarori musamman a fagen tattalin arziki.
A ci gaba da jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi ishara da batun ba da kariya wa haramin Imaman Ahlulbaiti (a.s) da kuma shahidan da suka ba da rayukansu a wannan tafarkin inda ya ce: Wannan lamarin yana daga cikin lamurra masu ban mamaki na tarihi ta yadda wani matashi daga Iran ko kuma daga wasu kasashe na daban, cikin imani da son ransu za su bar matansu da kananan yaransu da rayuwarsu ta jin dadi su tafi wata kasa ta daban don yin jihadi a tafarkin Allah, sannan kuma su yi shahada a bisa wannan tafarkin.
Jagoran ya bayyana gagarumin imanin da masu kare haramin Imaman suke da shi da kuma irin hakuri da juriyar iyalansu a matsayin wasu daga cikin bangarori masu ban mamakin wannan lamarin yana mai cewa: Wani bangare na wannan lamarin shi ne tsayin daka da kuma karfin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ta ginu bisa tushen imani, azama da iradar mutane muminai, mujahidai sannan kuma shahidai.
Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa har ya zuwa yanzu makiya tsarin Musulunci na Iran sun gaza wajen fahimtar tushen karfi da tsayin dakanta, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Shahidai da iyalansu su ne tushe da kashin bayan tsarin Jamhuriyar Musulunci, a saboda haka ne a koda yaushe tsarin ya sami nasara kan kalubale da barazanar da ya dinga fuskanta.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A duk inda muka riko da kuma dogaro da ruhi na juyin juya hali, lalle kuwa mun sami ci gaba. Sannan kuma a duk inda muka yi kasa a gwiwa don dadadawa ma'abota girman kai, to kuwa mun fuskanci koma da baya.
Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar wajibi ne tinkari makiya ma'abota girman kai da ruhi irin na tsayin daka da juyin juya hali, Jagoran ya bayyana cewar: imani da Allah, yarda da tafarkin jihadi da gagarumin ruhi na imani da juyin juya hali su ne tushen karfin tsarin Musulunci a fadar da yake yi da ma'abota girman kai. Duk kuwa da tasirin irin wannan karfin da suke gani, to amma sun gagara fahimtar hakikanin wannan lamari. A saboda haka ne suke dogaro da kuma bin tafarkin amfani da karfi da rashin imani.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana samar da kungiyoyin ta'addanci masu kafirta musulmi irin su kungiyar Da'esh (ISIS) a matsayin misalin amfani da wannan tafarki na rashin imani wajen fada da tsarin Musulunci na Iran, yana mai cewa: Babbar manufar samar da kungiyoyin ta'addanci masu kafirta musulmi da kuma irin danyen aikin da suke yi a Iraki da Siriya ita ce fada Iran. To sai dai karfin tsarin Jamhuriyar Musulunci ne ya tsare su a Iraki da Siriya da kuma tsaka mai wuyan da suke ciki.
Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar babu wani bambanci a wajen irin wadannan kungiyoyi na ta'addanci masu kafirta musulmi tsakanin Shi'a da Sunna, duk wani musulmin da yake tare da juyin juya halin Musulunci da kuma nuna kiyayya wa Amurka abokin gabansu ne, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da abubuwan da ke faruwa a kasar Bahrain inda ya ce: A kasar Bahrain ma lamarin ba shi ne batun Shi'a da Sunna ba, face asalin lamarin shi ne mulki na zalunci da wasu ‘yan tsiraru ma'abota girman kai suke yi wa mafiya yawan mutanen kasar.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin takurin da mahukuntan Bahrain suke yi wa babban malami mujahidin kasar Sheikh Isa Qasim a matsayin wata alama da ke nuni da wautarsu inda yace: Sheikh Isa Qasim dai shi ne mutumin da a duk lokacin da yake magana da mutanen Bahrain ya kasance yana hana mutane daukar makami a yunkurin neman hakkinsu da suke yi. To amma mahukuntan Bahrain sun gagara fahimtar cewa kai hari wa wannan malamin, yana nufin kawar da wannan garkuwar da take hana matasan kasar tinkarar gwamnatin kasar da duk wata hanyar da ta sawwaka musu.
Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar ma'abota girman kai da ‘yan amshin shatansu sun gagara fahimtar mutane da kuma imaninsu don haka suke kuskure wajen lissafin da suke yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ingantacciyar hanya, ita ce tafiya bisa tafarkin Musulunci da kuma dogaro da Allah Madaukakin Sarki. Sannan kuma al'umma ma'abociyar imani da tsayin daka ce kawai za ta iya yin nasara a kan abubuwan da suke kawo mata cikas da kuma samun ci gaba.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi dukkanin al'umma zuwa ga amfanuwa da dararen Lailatul Kadari da sauran ranakun da suka saura na watan Ramalana mai alfarma yana mai cewa: A wadannan darare da safiyarsu wadanda lokuta ne na tawassuli da kankan da kai a gaban Allah Madaukakin Sarki, wajibi ne ta hanyar neman daukin manyan bayin Allah ciki kuwa har da shahidai, mu yi kokarin addu'oi da neman taimakon Ubangiji Madaukakin Sarki.
Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da Hujjatul Islam wal muslimin Shahidi Muhallati, wakilin Jagora kana kuma shugaban cibiyar shahidai da masu sadaukarwa ta kasar Iran ya gabatar da jawabinsa, inda yayin da yake bayyana wajibcin sanar da matasa irin kokari da tsayin dakan da shahidai da masu sadaukarwa suka yi yayi karin haske kan irin ayyukan da cibiyar tasa ta yi a wannan bangaren.