Kamfanin
dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga shafin jaridar This Day ta habarta cewa
Al'ummar musulmi Almajiran shekh Ibarahim Yakoubu Al-zakzaky sun gudanar da
zanga-zangar raya ranar Qudus a jahohi daban daban na cikin kasar duk kuwa da
cewa Jagoran su da wasu mukarabansa na tsare a hanun hukuma.
Mahalarta Zanga-zangar a birnin katsina sun daga kwalye da kyallaye dauke da taken yin tir da zaluntar al'ummar Palasdinu da 'yan sahayoniya su ke yi.
A garin Potuskum da ke Jahar Yobe ma an sami dandazon masu zanga-zangar da su ka fito daga cikin birnin da kuma garuruwan da su ke kusa.
A Garin Kanon Dabo ma duban magoya bayan shekh Ibrahim Zakzaky ne suka gudanar da zanga-zangar bayan kamala sallar Juma'a
A kowace shekara dai harkar musulunci a karkashin Sheik Ibrahim Yakub al-zakzaky tana gudanar da zanga-zangar ranar qudus ta duniya daidai a ranar juma'ar karshe ta watan Ramadhan bisa amsa kiran jagoran juyin musulmi, Marigayi Imam Khumain.
A shekarar dubu biyu da sha hudu dakarun tsaron Najeriya sun kai farmki kan mahalarta zanga-zangar Qudus din a garin Zariya, inda suka kashe Mutane 33 daga cikin su a kwai 'ya'yan shekh Ibrahim zakzaky guda uku.