IQNA

Jagoran Juyi A Lokacin Sallar Idin Fetr:

Kokarin Kawata Abu Maras Kyau Shi Ne Babban Hadari Da Ke Bada mai Kyau

23:30 - July 07, 2016
Lambar Labari: 3480587
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah sayyid Khamenei a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar idin karamar salla ya yi hannunka mai sanda kan wajabcin yaki da duk wani aiki da ya sabawa shari'a a cikin harkar gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar yau Laraba ce miliyoyin al'ummar Iran a duk fadin kasar suka gudanar da sallar idin karamar salla bayan wata guda na azumin watan Ramalana mai alfarma. A birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ma, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ne ya jagorancin sallar idin da aka gudanar a Musallar Imam Khumaini (r.a) da ke birnin na Tehran.

A jawabin da ya gabatar a hudubar farko ta sallar idin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya taya al'ummar Iran da sauran al'ummomin musulmi na duniya murnar ranar idin, inda ya bayyana cewar azumin watan Ramalana na bana ya kasance cike da ababe masu kusata mutum ga Ubangiji da Kankan da kai ga Allah Madaukakin Sarki ga al'ummar Iran. Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne mu jami'an gwamnati mu faranta zukatan wadannan mutane muminai. Tabbas wajibi ne mu zamanto masu godiya ga Allah, amma a bangare guda wajibi ne mu san cewa muna da wani nauyi mai girman gaske a wuyanmu dangane da wannan al'umma.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar yadda al'umma suka dau azumi musamman matasa da samaruka shi din ma a irin wannan lokaci mai tsananin zafi, wani bangare ne mai kyau da faranta rai na watan Ramalanan wannan shekarar. Jagoran ya ci gaba da cewa: Koda yake wasu masu bakar aniya suna ta kokari wajen kwadaitar da matasa nesantar yin azumi, to amma cikin yardar Allah sun sha kashi, kuma a nan gaba ma ba za su yi nasara ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Yana da kyau mutane da jami'an gwamnati su fahimci irin tsare-tsare da bakar aniyar da makiyan kasar Iran suke da ita kan matasan kasar nan na nesanta su da addini. To amma sakamakon hikima da taka tsantsan din al'umma wannan shiri na su ya sha kashi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana gagarumin jerin gwanon Ranar Qudus ta duniya da aka gudanar a kasar Iran cikin tsananin zafin rana musamman a jihohin kudancin kasar a matsayin wani bangare mai kyau da faranta rai na watan Ramalanan wannan shekarar kana kuma daya daga cikin manyan ayyuka da kokarin da al'umma suka yi a watan Ramalanan, daga nan sai ya ce: Wannan gagarumar fitowa da al'umma suka yi da kuma nuna goyon bayansu ga lamarin Palastinu, a hakikanin gaskiya suna sanar da duniya ne cewa koda a ce wasu gwamnatocin kasashen musulmi za su ha'inci lamarin Palastinu ko kuma wasu gwamnatin za su yi kasa a gwiwa ko kuma wasu al'ummomin ba su da labarin abin da ke faruwa a kan al'ummar Palastinun, to amma al'ummar Iran kan a shirye suke su yi tsayin daka wajen tinkarar dukkanin don ci gaba da raya lamarin Palastinun.

Ayatullah Khamenei ya bayyana watan Ramalanan bana a matsayin wata alama mai girma da ke nuni da irin neman kusaci da Allah da mutane suke da shi. Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin majalisin karatun Alkur'ani mai girma da aka gudanar a wurare masu tsarki da suke kasar Iran wadanda kuma kafafen watsa labarai sun watsu su, Jagoran ya bayyana cewar: Wani bangare mai faranta ran shi ne irin tarurrukan shan ruwa da aka dinga shiryawa a garuruwa daban-daban musamman a unguwanni daban-daban na Tehran wanda haka wata alama ce ta son hidima ga mutane. A hakikanin gaskiya hakan lamari ne mai faranta rai ga kowa.

Jagoran yayi kakkausar suka ga irin tarurrukan shan ruwa da ake shiryawa da ake kashe kudi mai yawan gaske da kuma almubazzaranci wanda a cewarsa ana gudanar da su ne a kan mutanen da ba sa bukatar irin wadannan kayayyakin shan ruwa maimakon a ba wa mabukata.

A huduba ta biyu ta sallar idin, Ayatullah Khamenei yayi ishara da hare-haren ta'addancin da aka kai kasashen Iraki, Turkiyya, Bangladesh da sauran kasashe a baya-bayan nan yana mai cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa Idin karamar salla na bana ya zamanto wani lokaci na juyayi ga al'ummomin wasu kasashen sakamakon ayyukan ta'addancin wasu ‘yan ta'adda wadanda suke son su maye gurbin "Musulunci na hakika" da "Musulunci na jebu" don biyan bukatun iyayen gijinsu. Wannan danyen aikin kuwa ya samo asali ne sakamakon kirkiro irin wadannan kungiyoyi na ta'addanci da kungiyoyin leken asirin Amurka, Ingila da haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi ne.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewar laifin kashe mutanen da ba su ci ba su sha ba yana wuyan masu goyon bayan irin wadannan kungiyoyi na ‘yan ta'adda masu kafirta musulmi ne, duk kuwa da cewa su din ma a halin yanzu sun fara fuskantar cutarwar wadannan ‘yan ta'addan, to amma duk da hakan ba za a taba mancewa da wannan danyen aiki na su ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana fitina da yake-yaken da aka haifar a kasashen yankin nan irin su Siriya, Libiya da Yemen a matsayin babban abin bakin cikin, daga nan sai ya ce: Shekara daya da watanni uku kenan ake musu ruwan bama-bamai, to amma wajibi ne a jinjinawa wadannan al'ummar da jagororinsu ma'abota hikima, wadanda duk da irin wannan yanayin da suke ciki ga kuma tsananin zafin rana, to amma sun gudanar da gagarumin jerin gwanon Ranar Qudus ta duniya.

Haka nan yayin da yake bayyana cewar manufar ma'abota girman kan duniya na rura wutar yaki da rashin tsaro da ta'addanci a yankin Gabas ta tsakiya ita ce kokarin sanya a manta da lamarin Palastinu, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Gwagwarmaya don ‘yanto kasar Palastinu, wata gwagwarmaya ce ta Musulunci ta gaba dayan al'umma, wanda ci gaban hakan wani nauyi ne da ke wuyan dukkanin musulmi. Takaita lamarin Palastinu da kuma bayyana shi a matsayin wani lamari na larabawa kawai, babban kuskure ne.

A bangaren karshe na hudubar tasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da batun ta'annuti ga tattalin arzikin kasa da kuma yadda aka samu wasu jami'an gwamnati suna deban kudin baitul mali ba bisa ka'ida ba, inda ya kirayi shugaban kasa da sauran bangarori biyu na gwamnati, wato bangaren shari'a da majalisa da su yi fada da hakan da kuma halin ba sani ba sabo ga duk wani jami'in da aka same shi da hannu cikin wannan badakalar.

3513279

captcha