IQNA

Jagora A Yayin Ganawa Da Jami'an Gwamnati:
23:32 - July 07, 2016
Lambar Labari: 3480588
Bangaren siyasa, Ayatollah Khamenei jagoran juyin Islama ya bayyana a lokacin da yake ganawa da mayna jami'an gwamnatin kasar Iran cewa, babbar manufar Amurka ta haifar rikice-rikice a cikin kasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya ita ce a mantar da su batun Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarat cewa ya nanaklto daga shafin jagora cewa, da hantsin yau Laraba ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan jami'an gwamnati da wasu gungun jama'ar kasar Iran da kuma jakadun wasu kasashen musulmi da suke Tehran a yayin da suka kai masa ziyarar taya shi murnar zagayowar ranar karamar salla ta bana inda ya bayyana ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka a matsayin tushen yakukuwa, rashin tsaro da kuma ayyukan ta'addancin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya da sauran kasashen musulmi da nufin samar wa haramtacciyar kasar Isra'ila damar numfasawa da kuma mance batutuwa masu muhimmanci ga musulmi musamman batun kasar Palastinu. Daga nan sai Jagoran ya ce: Hanya guda kawai ta fada wannan makircin ita ce hakikanin fahimtar makiya na hakika da kuma tsayin daka wajen tinkararsu. Sannan kuma al'ummar Iran ta tabbatar da cewa hanya guda kawai ta samun ci gaba ita ce tsayin daka.

Yayin da yake isar da sakon taya murnar wannan rana ta idi ga al'ummar Iran da sauran al'ummomin duniya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da halin da ake ciki a duniyar musulmi na irin zubar da jinin mutane, rashin tsaro, tashe-tashen bama-baman da suke faruwa a yankin yana mai cewa: Daya daga cikin lamurra masu muhimmanci shi ne fahimtar tushen wadannan matsaloli da duniyar musulmin take fuskanta a halin yanzu da kuma wadanda suke kwadaitarwa da kuma yada ta'addanci a boye.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin yadda dukkanin kasashen duniya da kuma manyan kasashen duniya suke bayyana barrantarsu a fili ga ayyukan ta'addanci da kuma kafa hadaka ta karya da sunan fada da ta'addanci, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Sabanin ikirari na zahiri da manyan kasashen duniya suke yi, amma a aikace suna goyon baya da kuma kwadaitar da ta'addancin ne.

Haka nan yayin da yake magana kan yadda jakadar Amurka ya kasance cikin masu zanga-zangar kasar Siriya a farko-farkon ranakun rikicin kasar da kuma yadda ya dinga share fagen rikici da yakin basasa a kasar, Jagoran ya bayyana cewar: Wadannan mutanen sun mayar da rani rikici na siyasa zuwa ga rikici na zubar da jinni, sannan daga baya kuma ta hanyar ba da goyon baya na kudi da makamai, suka ci gaba da dauko mutane daga kasashen waje da turo su zuwa kasashen Siriya da Iraki don su samar da rashin tsaro da irin matsalolin da a halin yanzu ake fuskanta.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da jaddadawar da ya sha yi na cewa dangane da irin kiyayyar da Amurka take nuna wa al'ummar Iran, Jagora yayi ishara da abubuwan da Amurkan ta dinga yi wa Iran tsawon shekaru 37 din da suka gabata don haka sai ya ce: Ton ranar farko na nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran, Amurka ta daura damarar kiyayya da marigayi Imam Khumaini (r.a) da wannan gagarumin yunkuri nasa, wanda har zuwa yau din nan suna ci gaba da wannan kiyayyar. To amma sakamakon fadaka ta al'umma da kuma taka tsantsan da shirin da gwamnati da jami'an gwamnati suke da shi, wannan kokari na Amurkan ya zama aikin baban giwa.

Haka nan kuma yayin da ya ke jaddada cewar al'ummar musulmi suna bukatar sanin makiyi da kuma fahimtar irin makirce-makircensa, Jagoran ya bayyana cewar: Wani misalin na kokarin mai da rikici na siyasa zuwa ga yakin basasa shi ne abin da ke faruwa a kasar Bahrain.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai ba ta sanya bakinta cikin rikicin kasar Bahrain kuma a nan gaba ma ba za ta yi ba. To amma idan har akwai hikima da fahimta mai kyau ta siyasa a kasar bai kamata su bari rikici na siyasa ya koma zuwa ga yakin basasa ba, sannan kuma bai kamata su yi fada da mutane ba.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa babbar manufar manyan kasashen duniya ma'abota girman kai karkashin jagorancin Amurka na haifar da rikici da fadace-fadace a yankin nan ita ce mantar da al'umma matsalar Palastinu. Daga nan sai ya ce: Suna so ne su yi inkarin samuwar wata la'umma a wani yanki na duniya, alhali kuwa Palastinu wata kasa ce mai tsohon tarihi na shekaru dubbai. Haka nan kuma al'ummar Palastinu su ne ma'abota wannan kasa, ba kuwa za su iya inkarin wannan hakikar ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa za ta fuskanci matsala da sakamakon irin zaluncin da take yi wa al'ummar Palastinu.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Matsalar Palastinu ita ce babbar matsalar duniyar musulmi. A saboda haka babu wata kasar musulmi da ma wacce ba ta musulmi ba amma dai mai lamiri irin na ‘yan'adam da za ta mance da wannan batu.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi ishara da batun kasar Yemen da irin ruwan bama-baman da ake ci gaba da yi musu a masallatai, asibitoci da gidajensu yana mai cewa: Wajibi ne masu wuce gona da irin su kawo karshen wannan wuce gona da iri na su, sannan kuma wajibi ne kasashen musulmi su ladabtar da wannan mai wuce gona da irin wanda ya fake da wani dalilai mai rauni maras tushe wajen aikata wannan danyen aiki nasa.

Yayin da kuma yake ishara da tsayin dakan al'ummar Iran, Jagoran cewa yayi: Nasarorin da al'ummar Iran ta samu sun samo asali ne sakamakon tsayin dakan da suka yi. Idan kuwa da a ce al'ummar ta mika kanta ga masu tinkaho da karfi na duniya, da kuwa ba ta sami irin ci gaban da ta samu a yau ba.

Jagoran ya bayyana "tsayin daka da gwagwarmaya, karfafa yanayin cikin gida, irada da kishin kasa da kuma dogaro da Allah" a matsayin tushen ci gaba, don haka sai ya ce: Matukar al'umma sakamakon imanin da take da shi ta tsaya kyam sannan ba ta dogara da kowa ba face Allah Madaukakin Sarki, sannan kuma ba ta tsoron kowa sai Allah, to kuwa za ta kai ga asalin manufar da take son cimmawa.

Kafin jawabin Jagoran, sai da shugaban kasar Iran, Hujjatul Islam wal muslimin Hasan Ruhani ya gabatar da jawabinsa inda ya taya al'ummar musulmi murnar wannan rana mai albarka. Har ila yau kuma ya bayyana rashin tsaro, ayyukan ta'addanci da kuma yawaitar ‘yan gudun hijira a matsayin wasu daga cikin manyan matsalolin duniyar musulmi don haka sai yayi kiran da a kafa wata hadaka ta hakika don fada da ta'addanci da kuma tsaurin ra'ayi.

Shugaba Ruhani ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran kamar yadda ta saba za ta ci gaba da hada kai da aiki tare da sauran kasashe don magance matsalolin kasashen musulmi sannan kuma ba za ta taba watsi da wadannan al'ummomi ba.

3513324

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: