IQNA

Jami’an Tsaron Bahrain Sun Afkawa Masu Goyon Bayan Ayatollah Isa Qasem

23:47 - July 10, 2016
Lambar Labari: 3480596
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Bahrain sun afka kan masu jerin gwanon nuna goyon baya ga babban malamin addini na kasar Ayatollah Isa Qasem.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’at Bahrain cewa, jami’an tsaron yan sanda kasar Bahrain a cikin kayan sarki sun afka kan masu jerin gwanon nuna goyon baya ga Ayatollah Isa Qasem babban malamin addini na kasar.

Bayanin ya ce masu gangamin sun daga kyallaye da kuma rera taken nuna goyon baya ga malamin, da kuma yin Allawadai da janye izinin zama dan kasa daga gare shi.

Haka nan kuma yan sanda sun yi amfani da kulake da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu gudanar da gangamin.

Mahukuntan kasar ta Bahrain sun dauki mataklan takurawa ga mabiya mazhabar iyalan gidan amnzo a kasar, inda suke cin zarafin mutane babu kakautawa.

Daga cikin irin matakan kuwa har da matakin janye izinin zama dan kasa daga Ayatollah Sheikh Isa Qasem babban malamin addini mafi karfin fada aji kasar, kamar yadda kuma kafin nan sun rusa babbar jami’ar siyasa ta kasar wato Alwifagh, tare da rusa babbar majalisar malaman kasar.

3513929

captcha