IQNA

23:26 - July 27, 2016
Lambar Labari: 3480650
Bangaren kasa da kasa, a yau ne kotun masaratar kama karya ta Bahrain ta gudanar da zamanta kan shar’ar Ayatollah Isa Kasim amma an dage zaman zuwa 14 ga Agusta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alalam cewa, a yau ne Laraba kotun masaratar kama karya ta Bahrain ta gudanar da zamanta kan shar’ar Ayatollah Isa Kasim bisa zrginsa da tara kudade ba bisa kaida ba, sai an dage zaman zuwa 14 ga watan Agusta mai kamawa.

A jiya talata kotun hukunta manya laifuka ta kasar Bahrain ta sanar da fara sauraren karan Shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahren Shekh Isa Kasim wanda ake zarki da laifin tunzura Al'umma wajen yiwa Gwamnati tawaye a gobe Laraba.

Kafin wannan sanarwa Al'ummar yankin Adderaz na birnin Manama sun taru a gaban kotun domin neman kotun da ta sanya ranar sauraren karar na shekh Isa Kasim.

Gwamnatin ta Bahrain na ci gaba da kamen manya-manyen malimai mabiya mazhabar Shi'a da kuma dukkanin wani Dan siyasa ko kuma babban mutun dake adawa da siyasar ta.

A bangare guda, kungiyoyin kasar dake adawa da bakar siyasar masarautar Ali khalifa dake zaune a kasashen waje sun bukaci kungiyoyin kasa da da kasa da kasashen masu 'yanci na Duniya da su dauki matakin gaggawa domin kawo goyon bayansu ga Al'ummar kasar Bahrain.

Sun dai ayyana ranar juma'a ashirin da tara ga wannan wata na Yuli shekarar dubu biyu da sha shida a matsayin ranar goyon bayan Al'ummar kasar Bahrain da suke fuskantar bakin zalunci daga mahukuntan kama karya na kasar.

3518294

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: