IQNA

An Soma Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A Gambia

23:31 - July 27, 2016
Lambar Labari: 3480652
Bangaren kasa da kasa, an soma gasar kur’ani mai tsarki ta duniya a kasar Gambia karkashin shirin shugaban kasar Yhya Jame tare da halartar wakilan kasashe 28 na duniya.
Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Obsever cewa, wannan gasa an shiryata ne domin tunawa da juyin mulkin shekara ta 1994 da aka yi a kasar.

An bude gasar ne tare da halartar manyan jami’an gwamnatin kasar, da suka hada da ministoci da kuma malaman addini da na jami’oi gami da wakiln kasashen ad suke halartar gasar, kamar yadda kuma aka gabatar da jawabai kan manufar shirya wannan gasa.

Fatu Lamin shi ne ministan ilimi maras zurfi a kasar, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa agaban taron bude gasar ta kasa da kasa ya bayyana cewa, babban burinsu na shirya wannan gasa shi ne ci gaba da raya kr’ani da kuma koyarwarsa atsakanin al’ummar musulmi.

Ya ci gaba da cewa babban abin takaici ne yadda wasu suke yin amfani da ayoyin kur’ani mai tsarki wajen cimma burinsu na bata sunan addini a idon duniya, inda ya ce ‘yan ta’adda suna fakewa da wasu ayoyin kur’ani ne domin ta’addancisu.

Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya kan malaman addini kan su wayar da kan musulmi musamman ma matasa kan hakikanin koyarwar kur’ani da kuma manzon Allah (SAW) domin kauce wa fadawa cikin mummunar fahimta da kuma yaudarar ‘yan ta’adda.

Kasashe 28 da suke halartar gasar sun hada da Afghanistan, Kamaru, Chadi, Lebanon, Tunisia, Yemen, Burkina Faso, Ivory Coast, Najeriya, Nijar, Jordan, Malaysia, Mali, Palastinu, Pakistan, Oman, Senegal, Somalia, Turkiya, Uganda, Qatar, Mauritania, Benin da kuma ita ksar ta Gambia.

Alkalan gasar sun fito ne daga kasashen Morocco, Turkiya, Senegal, Masar, Lebanon da kuma Gambia.

3518141

captcha