IQNA

22:16 - July 31, 2016
Lambar Labari: 3480666
Bangaren kasa da kasa, Joko Widodo shugaban kasar Indonesia ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a samu jami’ar musulunci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Jakarta Post cewa, Widodo ya bayyana a lokacin da yake bude gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya cewa, yana fatan nan ba da jimawa ba za a samu jami’ar musulmi wadda za ta rika koyar da ilmomin kur’ani da addini mai zurfi.

Ya ci gaba da cewa, tun kafin wannan lokacin ya dace a samar da jami’a mai zaman kanta, wadda za ta rika koyar da ilmomin kur’ani mai tsarki da kuma sauran bangarori na addini, amma hakan ba ta samu, duk kuwa da cewa yana da burin ganin an aiwatar da hakan na ba da jimawa ba.

Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a matsayi na kasa baki daya, inda take samun haartar wakilai daga dukkanin lardunan kasar, kuma shi ne karu na 26 da ake gudanar da wannan gasa ta kasa baki daya.

Kimanin wakilai dubu 5 ne daga larduna 34 na kasar ta Indonesia suke halartar wannan gasa, da suka hada da makaranta da kuma mahardata, gami da wadanda ska kware a bangaren tafsiri da kuma sanin hukuncin karatun kur’ani mai tsarki.

Za a bayar da kyatuka na musamman daga karshe ga wadanda ska nuna kwazoa awannan gasa.


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: