IQNA

Shafin Olympic Ya Ce:

Kimiya Alizadeh Da Hadaya Wahbah Sun Daga Tutar Mata Musulmi

23:45 - August 20, 2016
Lambar Labari: 3480727
Bangaren kasa da kasa, shafin yanar gizo na wasannain motsa jiki na Olympic na shekarar 2016 ya bayyana rawar da mata musulmi suka taka a bangaren taekwondo wanda hakan ke nufin ci gaba ta fuskar wasanni a tsakanin mata musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Rio2016.com cewa, Kimiya Alizadeh mai wasan taekwondo daga kasar ta bayar da mamaki matuka dangane da irin rawar da ta taka a wajen gasar ta motsa jiki a wannan karo a nauyin kg 57.

Wannan matashiya ‘yar shekaru 18 ta karni lambar yabo ta zinariya, kuma ta bayyana cewa ta mika wannan lamabr yabo ga dukkanin mata na kasar Iran, kamar yadda kuma take kara karfafa gwiwarsu a harkokin wasanni.

Kamar yadda kuma ta bayyana godiyart ga Allah a lokacin da ta samu wannan nasara, inda ta yi sujada anan take tana farin ciki da wannan baiwa da Allah madaukakin sarki yay i mata da kuma nasarar da ta samu.

Wannan dai shi ne karon farko da wata musulma kuma yar kasar ta Iran wadda take sanye da hijabi ta samu nasarar daukar wannan lamba ta daya a wasannin motsa jiki na duniya.

Hadaya Wahba ita ma’yar kasar Masar ce wadda ta taka rawar gani tana sanye da hijabi na muslunci, wanda hakan ke nuni da cewa mata musulmi za su iya taka rawa a wannan bangare tare da kiyaye kaidoji da koyar ta addinin muslunci.

3524010

captcha