IQNA

Zama Kan Al’adun Muslunci Karkashin Shirin Iran

23:51 - August 20, 2016
Lambar Labari: 3480729
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro wanda ya shafi yada al’adun muslunci a mahangar mayna malamai wanda karamin ofishin jakadancin Iran ya shirya a Tunis.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin yada al’adun muslunci na kasar Iran a Tunisia cewa, zaman taron zai gudana ne a bangaren da ya shafi yada al’adun muslunci a mahangar manyan malamai irin su Imam Khomeni (RA) da sheikh Muhammad Khidr Hussain wanda karamin ofishin jakadancin Iran ya shirya a Tunis fadar mulkin kasar.

Tarion zai fara ne da lacca daga shugaban ofishin yada al’adu na kasar Iran Muhammad Asadi Muwahhad, kamar yadda kuma msana za su gabatar da jawabai daban-daban kan wannan batu.

Babbar manufa shirya wannan taron dai ita ce raya mahangar wadannan manyan malami Imam Khomeini (RA) da kuma Sheikh Muhammad Khidr Hussain.

Sheikh Muhammad Khidr Hussain an haife shi ne a cikin shekara ta 1873 a kasar Tunisia,kuma ya yi karatu a jami’ar zaituna, kamfin daga bisani ya bar kasar.

Ya yi yaki da yan mlkin mallaka faransa a kasar Tunisia, amam daga bisani ya tafi birnin Damascud na Syria, daga bisani kuma ya koma Alkahira.

Wannan babban malami dan kasar Tunisia ya rike shugabancin jami’ar Azhar, kuma ya rasu a cikin shekara ta 1981 a birnin Alkahira, ya bar littafai kimanin 20 da ya rubuta.

3523956

captcha