IQNA

Wata Kotu A Kenya Ta Ce Dalibai Suna Iya Saka Hijabi

19:33 - September 10, 2016
Lambar Labari: 3480772
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Kenya sun bayyana cewar wata kotun daukaka kara a kasar ta bayyana cewar dalibai mata musulmi a kasar suna iya sanya hijabi a lokacin da za su tafi makarantun na su a matsayin tufafin makarantar.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yana gizo na Anatoli cewa, a cikin hukuncin da kotun ta fitar ta ce musulmin suna da damar sanya hijabi su tafi makarantun su, kamar yadda kuma ta bukaci hukumar kula da ilmi ta kasar da ta tsara wasu sabbin dokoki dangane da tufafin 'yan makarantar wadanda ba za su nuna wariya ko cutarwa ga wani dalibi saboda addininsa ba.

Hukuncin kotun daukaka karar dai ya biyo bayan wani hukunci ne da wata kotu a kasar ta yanke a kwanakin baya inda ta haramta wa 'yan makaranta mata musulmi sanya hijabi din yayin da suke makarantar, lamarin da kotun daukaka karar ta ce babu laifi cikin hakan.

Batun haramcin sanyan hijabi a makarantar dai ya biyo bayan karar da wata makaranta ta kiristoci a kasar ta shigar ne inda ta bukaci da a hana 'yan mata musulmi sanya hijabi din don a cewarsu sanya kaya daban-daban tsakanin daliban zai haifar da rashin jituwa da kyamar juna tsakanin daliban.

3529115


captcha