Kamfanin dillancin labaran kur’ani
na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na
Bernama cewa, an fara aiwata da shirin ne a yau daga kimanin karfe 9 na safe a
lokacin tsayuwar Arafa, inda ake karanta kur’ani mai tsarki surat Hajj.
Wannan shiri dai wani kamfanin a kasar Malaysia ne ya kirkiro shi, da nufin karfafa lamarin kur’ani mia tsarki da kuma girmama aikin ibada ta hajji da ake gudanarwa a wannan rana kuma awannan lokaci.
Shirin ya samu karbuwa daga sassa daban-daban na muuslmin duniya, domin kuwa an yi ta bayani a shafukan yanar gizo tun kafin lokacin, kuma miliyoyin musulmi sun gani tare da nun agoyon bayansu.
A yau ne kimanin mahajjata miliyan daya da rabi da suka fito daga kasashen duniya daban-daban suke tsayuwar Arafa a wajen birnin Makka mai alfarma, dubban daruruwan musulmi maniyyata daga wasu kasashen ba su samu damar zuwa safke farali ba a shekarar bana, sakamakon rashin samun izinin shiga kasar daga masarautar iyalan gidan Saud da ke rike da madafun iko a kasar.