IQNA

Zaman Taro Mai Taken Kyamar Musulmi A Girka

20:18 - September 17, 2016
Lambar Labari: 3480789
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Buzusaki da hadin gwaiwa da cibiyar matasa a Girka za su gudanar da taro kan kyamar musulmi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Athens.icro.ir cewa, cibiyar Buzusaki tare da hadin gwiwa da kungiyar matasa ta Youthne Hellas za su gudanar da zaman taro ma taken No Hate Speech Movement.

Cibiyar sayar da littafai ta Free thinking zone na da hannu wajen shirya taron wanda zai guda da kimanin karfe 18:30 agogon kasar.

Wanann zaman taro dai zai hada da manyan masana da kuma jami’an diplomasyya gami da wasu fitattun marubuta da kungiyoyi masu zaman kansu, da kuma shugaban kungiyar musulmi ta kasar Yunus Muhammadi wanda zai gabatar da jawabi.

Babban abin da taron zai duba shi n yadda matsalar kyamar musulmi take kara kamari a kasar sakamaon abibuwan da ake yada na kin musulmi a wasu kasashen turai, tare da fayyace hakikanin abin da yake faruwa, da kuma banbance tsakanin muslunci an hakika da musluncin ‘yan ta’adda wanda baya da tushe a cikin mslunci na hakika, wanda akidar wahabiyanci ne tushensa ba koyar musulunci na hakika ba.

3530680


captcha