Bayanin y ace yanzu haka akwai alhazai da ba a san duriyarsu ba, kuma dukkaninsu alhazai wadanda suke da alaka da masu fafutuka da neman ‘yancin alummar Bahrain, wadanda Saudiyya ke kallonsu a matsayin hadari ga masautar Bahrain.
Haka nan kuma jawabin ya yi ishara da yadda hakan ke nuni da cewa a halin yanzu haramomi biyu bas u da aminci, sabanin yadda musulunci ya bayyana su, inda iyalan Saud ke amfani da su domin cimma bakaken manufofinsu na siyasa.
Tun bayan da aka fara gudanar da aikin ne dai aka nemi alhazai sama da ashirin na kasar Bahrain aka rasa inda suke, amma daga bisani mahukuntan saudiyyah sun sanar da cewa sun kame wasu alhazai da suka shiga kasar ab bisa doka ba, ba tare da wani Karin bayani ba.
Su ma a nasu mahukuntan Bahrain wadanda suke aiwatar da manofofin masarautar iyalan gidan Saud sun yi gum da bakunansu kan lamarin, bas u uffan kan rashin ganin alhazan kasar ba, wanda hakan ke nuni da cewa akwai wata Magana a tsakaninsu da mahukuntan Saudiyya.
Matasan sun bukaci al’ummar musulmi da su karbe lamarin tafiyar da aikin hajji daga hannun yayan Saud, wadanda suke mamaye da wurare masu tsarki mallakin dukkanin muuslmi na duniya baki daya, tare da tafiyar da su bisa siyasarsu.