IQNA

Hukuncin Daurin Makonni 2 Kan Wanda Ya Wulakanta Kur’ani A Amurka

23:09 - October 07, 2016
Lambar Labari: 3480833
Bangaren kasa da kasa, kotun kasar Amurka ta yanke hukuncin daurin makonni biyu rak kan wani dan kasar da ya kone kur’ani.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaqna cewa, wata kotu a kasar Amurka ta yanke hukuncin daurin makonni biyu kan wani dan kasa mai suna Adam David Smoke wanda ya yi rubutun batunci kan bangae wata cibiyar muslunci a kasar a shekara ta 2011.

Saurayin dan shekaru 24 da haihuwa a lokain da ya aikata wannan ta’aa, ya amsa cewa ya aikata abin da ake tuhumarsa, kuma kotu ta yanke hukuncin dauri na makonni biyu a kans a cikin garin Spring Field, domin ya zama darasi gareshi da ma masu akata hakan, kamar yadda zai bayar da tara ta daka dubu 10 da 440, da aikin wahala na sa’oi arbain.

A cikin watan Yunin shekara ta 2011 ce dai aka samu wannan mutum da aikata wannan laifin, yanzu haka kuma ana ckin batun ganin an samar da wani yanayi wanda zai hana aikata irin wanann rashin sanin ya kamata akan musulmi da ma duk wasu masu addini da ake cutarwa saboda addininsu a kasar.

Abin tuni a nan da shi ne tun a cikin watan na Yuni ne dai wani alkalin otun Amurka, ya yanke hukunci kan abokin aikata wannan ta’asa na smoke wato Jushua Samuel, wanda tare ne suka kaddamar da farmaki kan masallaci tare da tsorata masallata, an kuma ci sa tarar dala dubu biyar da da 220, da aiki whala na tsawon saoi 20 a matsayin ladabtarwa.

3536117


captcha