Taron ya samu halartar wasu daga cikin fitattun 'yan siyasa na kasar ad suka hada da Gharib Bilal tsohon mataimakin shugaban kasa, da kuma sheikh Alhadi shugaban kwamitin sulhu na kasa tsakanin musulmi da kuma mabiya addinin kirista, da kuam wasu daga cikin jakadun kasashen ketare da ke wurin.
Mahdi Agha Jafari a lokacin da yake gabatar da jawabinsa agaban taron ya bayyana cewa, batun Quds da kuma halin da yake ciki na mamaya a hannun yahudawa shi ne abu mafi muhimamnci da ke gaban musulmia halin yanzu.
Ya kara da cewa Isra'ila ita ce babbar matsala a halin yanzu ga musulmi da ma sauran al'ummomi duniya, inda take kan gaba wajen haifar da rikici a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
Agha Jafari ya ce an sha shirya zama kan matsalar palastinu da kuma zaluncin da al'ummarta ke fuskanta daga yahudawa amatsayi na kasa da kasa, amma har yanzu babu wani abin da ak aiya cimmawa kan hakan.
Daga karshe yay aba da irin rawar da gwamnatin kasar Tanzania da kuma al'ummar kasar suke takawa wajen ganin an samu fahimtar juna da zaman lafiya atsakanin dukkanin mabiya addinai da suke kasar.