IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Sabbin Muslunta A Dubai

23:51 - October 21, 2016
Lambar Labari: 3480871
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta sabbin muslunta a birnin Dubai.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wam cewa, an kammala dukkanin shirye-shirye na gudanar da gasar kur’ani ta sabbin musluta a Dubai.

Wannan gasa dai za ta kebanci mutanen da suka karbi muslunci ne da suke zaune a birnin Dubai, wadan da kuma sun fito ne daga kasashehn duniya daban-daban.

Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da sauran shirye-shirye, da hakan ya hada yin rijista da kuma tantance sunayen wadanda za su shiga gasar.

A kan gudanar da irin wannan gasa dai a kowace shekara wadda wata cibiyar gudanar da ayyukan alkhairi ta kasar kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, wanda kuma shi ne na farko da za a gudanar da ita da irin wannan salo.

An sanar da cewa mutanen da suka zo na farko zuwa na goma za su samu kyautar kudade da suka dirham dubu 50 na kasar hadaddiyar daular larabawa.

3539469


captcha