IQNA

Janye Takardar Dan Kasa Daga Babban Malamin Tafsiri A Pakistan

23:20 - October 22, 2016
Lambar Labari: 3480874
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Pakistan sun janye takardun zama dan kasa daga wasu malami a kasar lamarin da ya jawo fushin jama’a.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya bayar da rahoto daga kasar Pakistan cewa, daruruwan malamai ne da suka hada da sunna da kuma shi’a aka janye izinin zama dan kasa daga gare su bisa zargin yada tsatsauran ra’ayi.

Haka nan kuma wannan hukunci ya hada har da rufe asusun ajiyarsu na bankuna.

Duk kuwa da cewa akasarin malaman da wannan lamari ya shafa malaman sunna ne, amma akwai wasu daga cikin malaman shi’a da lamarin ya shafa, da suka hada har da Maksud Dumki sai kuma sheikh Mohsen Ali Najafi, babban malamin tafsirin kur’ani mai tsarki, kuma shugaban makarantar Jami’ul muntazar.

Chohdari Nisar Ali Khan ministan harkokin cikin gidan kasar ta Pakistan ya bayyana cewa, zato mafi karfi shi ne gwamnati za ta janye wannan matsaya da ta dauka.

Tun bayan da gwamnatin ta sanar da wannan hukunci, dubban jama’a suke ta gudanar da jerin gwano domin nuna rashin amincewarsu da abin da aka yi, tare da neman gwamnati da ta janye wannan hukunci da gaggawa.

3539867


captcha