Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya
nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na huffingtonpost cewa an gudanar da
wannan jin ra’ayin jama’a ne tsakanin al’ummar kasar Australia a garin Malborn,
birnin na biyu girma a kasar, inda kasha 58 na wadanda aka ji ra’ayinsu, suka
bayyana gamsuwarsu da barin ‘yan gudun hijira su shiga kasar.
Wannan jin ra’ayin jama’a da aka fitar da sakamakonsa yau Talata ya nuna cewa, adadin amsu son bar yan gudun hijira a tsakanin yan kasar Australia ya karu ne da kashi 7, idan aka kwatanta da jin ra’ayin da aka gudanar a shekarar da ta gabata, inda a lokacin kasha 49 na mutanen kasar suna bukatar a hana baki yan gudun hijira shiga kasar.
Sakamakon yaduwar ayyukan ta’addanci da sunan musulunci, hakan ya sanya kyamar musulmi na karuwa a kasashen turai, yayin da a kasar Australia lamarin yake raguwa.
Ana sa ran adadin musulmi zai dubu 700 a kasar Australia a cikin shekara ta 2030.