Ya ce babbar manufarsu ita ce yin amfani da hakan domin jawo hankulan sauran musulmi na duniya domin su goyi bayan kisan kiyashin da suk eyi kan msuulmi a Yemen bisa hujjar cewa an kai hari a Makka, alhali sun kwashe shekaru biyu suna lugudan wuta a Yemen ba tare da sun taba bayyana hakan a matsayin laifi ba.
Ya kara da cewa da yake ba su da gaskiya, sun kasa nuna inda suka ce harbor makamin da aka harba zuwa Makka, alhali Jidda da Makka garuruwa ne biyu mabnbanta, kuma akwai hotuna da suke inda makamin ya safka a Jiddah, wanda su ba su nuna haka, amma wadanda suka dauki hotunan a Jidda sun sanya a yanar gizo kowa zai iya gani, lamarin da ke karyata mahukuntan masarautar 'ya'yan gidan Saud.