IQNA

21:23 - November 04, 2016
Lambar Labari: 3480907
Bangaren kasa da kasa, Ministan mai kula da harkokin addini a kasar Tunisia ya rasa kujerarsa sakamakon kakkausar sukar da ya yi a jiya a kan akidar wahabiyanci da kuma tushensa.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa,kafofin yada labarai da dama na kasar Tunisia sun bayar da rahoton cewa, a yau Firayi ministan kasar Tunisia Yusuf Shahid ya fito ya bayyana cewa an safke minista mai kula da harkokin addini na kasar Abduljalil Bin Salim, sakamakon kalaman da ya yi, inda ya ce hakan ya saba wa tsarin diplomasiyyah na kasar.

A jiya ne ministan mai kula da harkokin addini na Tunisia Abduljalil bin Salim ya fito ya bayyana cewa, tushen duk wani ta'addanci da duniya take gani a halin yanzu da sunan addini Saudiyyah ce, kuma tushen akidar kafirta musulmi ya samo asali ne daga akidar wahabiyanci wanda wannan masarautar ce take yada wannan akida a duniyar musulmi a halin yanzu.

Ya ce baya gaba da Saudiyya a matsayinta na kasa, amma bai amince da salon tsarin mahukuntanta ba, saboda hakan ne ya jawo matsaloli da dama a duniyar musulmia halin yanzu, da hakan ya hada da yaduwar kungiyoyin ta'addanci a cikin kasashen musuulmi, saboda 'yan ta'addan da suka tasirantu da akidar wahabiyanci suna kallon kowa kafiri ne matukar dai bai yi riko da irin akidarsu ba, a kan haka ba su wata tantama wajen kashe musulmi ko tayar da bam su kashe tsakiyar mata da kanan yara, kuam suna ganin addini suke yi, saboda abin da aka dora su a kansa kenan.

Bin Salim ya ce ya zanta da manyan jami'an Saudiyya da suka hada da wasu daga cikin ministocin kasar, inda ya bukaci da su gyara tsarinsu na koyarwa, su sanya ido kan abin da ake koyar da daliban da ake yayewa a makarantun addini na kasar, domin sau tari su ne suke yada duk wata fitina a cikin kasashen musulmi.

Wannan furuci dai shi ne irinsa na farko da aka taba ji daga bakin wani babban jami'i a cikin gwamnatin Tunisia.


3543293

 


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: