IQNA

22:49 - November 05, 2016
Lambar Labari: 3480911
Bangaren kasa da kasa, kasar Kenya na shirin daukar bankuncin bababn baje koli na kayan abincin Halal.

Kamfanin dillancion labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga standard media cewa, a cikin makonni biyu masu zuwa ne za a gudanar da wani baje kolin kayan abincin halala a kasar Kenya wamda zai guda a Nairobi babban birnin wannan kasa tare da halartar kamfanonin kimanin 300 na ciki da wajen kasar.

Samar da kayan abincin halal yana daya daga cikin muhimamn hanyoyi da kamfanoni suke amfani da shi a halin yanzu na muslmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Daga cikin abubuwan da ya knsa kuwa har da bayar da inshore ga masu saka hannayen jari a ciki, kamar yadda kamfanoni da dama suna hada kai da sauran kamfanonin musulmi domin gudanar da aikin samar da kayan halal a cikin kasashen duniya, saboda amfani musulmi.

Kasar Kenya tana daga cikin kasshen da suke samun masu yawan shakatawa daga kasashen duniya, kuma hakan ya hada hara da musulmi, wanda kuma skan bukaci samun abin halal a duk inda suka safka, duk kuwa da cewa mafi yawan al’ummar kasar ba musulmi ba ne.

A cikin shekara ta 2008 kasar Kenya ta karbi bankunan musulunci da dama, wadanda suka zo suka bude rassa a cikin kasar, wanda hakan ya baiwa musulmi damar yin hada-hadar kudade a kasar Kenya ba tare da wata matsala ta banki ba.

Yanzu haka musulmi su ne kusan kasha daya bisa uku na dukkanin al’ummar kasar Kenya, inda adadainsu ya kai miliyan 10 a cikin miliyan 30 na kasar.

ASyyukan samar da abincin halal na daga cikin hanyoyin samu kudade ga kamfanoni a halin yanzu, inda kowa kan shiga cikin lamarin domin amfanin kansa.

3543423


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، kenya ، Nairobi ، Halal ، musulunci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: