IQNA

19:54 - November 08, 2016
Lambar Labari: 3480921
Bangaren kasa da kasa, masu tsananin kyamar musulunci sun kai hari kan wani masallaci a unguwar Ringby da ke cikin birnin Stockholm fadar mulkin kasar Sweden.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly cewa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai harin a kan wannan masallaci, wanda yake hade da wata babbar cibiyar musulunci, inda suka yi barna tare da farfasa tagogi da lalata wasu kayayyakin masallacin, kuma suka tsere ba tare da kame ko daya daga cikinsu ba.

A nasu bangaren mahukuntan kasar ta Sweden sun bayyana rashin jin dadi dangane da faruwar lamarin, a daidai lokacin da jami'an tsaro suka sanar da cewa sun shiga gudanar da bincike kan lamarin, da zimmar kame duk wadanda suke da hannu a cikin wannan aika aika, domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Kimanin musulmi dubu 400 ne dai suke rayuwa a cikin kasar Sweden, kuma ba su cika fuskar matsaloli irin wadannan ba daga jama'ar gari, sai bayan da aka fara samun hare-haren ta'addanci daga 'yan takfiriyyah a cikin kasashen turai.

3543994


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: