IQNA

23:38 - November 13, 2016
Lambar Labari: 3480936
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar Republican sun ziyarci wani masallaci na musulmi a garin Starling da ke cikin jahar Virginia.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nbcwashington cewa, wasu daga cikin shugabanin jam’iyyar Repubkican sun kai ziyara a masallacin ne a lokacin sallar azuhur, inda suka yi Magana da musulmi da suka taru a wurin kan zaben Trump a matsayin shugaban Amurka.

‘Yan siyasar sun kirayi musulmi da su kwantar da hankulansu, musamman ma yadda suke nuna damuwa kan zaben na Trump, bisa la’akari da kalaman da ya yi a lokacin yakin neman zabe, inda suka ce Trump ba zai kori musulmi ko takura msuu ba, domin kuwa daya daga cikin manufofinsa bayan lashe zabe shi ne hada kai da dukkanin mabiya addinai da hakan ya hada har da musulmi domin yin aiki tare.

John Wetback shugaban jam’iyyar Republican na jahar Virginia wanda ya lasancea cikin tawagar da ta ziyarci masallaciun ya bayyana cewa, musulmi kamar sauran dukkanin addinai suna da ‘yancin su yi addininsu ba tare da wani ya takura msuu ba, kuma a karkashin mulkin Trump musulmi za su ci gaba da kasancewa da wannan hakkin da suke da shi kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Ridha Jaka babban sakataren kwamitin masallacin ya bayyana wa ‘yan jam’iyyar ta Republican cewa, musulmi suna son zaman lafiya tsakaninsu da kowa, kuma suna fatan zaben na Trump ba zai kawo wata matsala ta kyamar musulmi da nuna musu wariya ba.

3545504


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، Virginia ، ziyarci ، masallaci ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: