IQNA

22:37 - November 14, 2016
Lambar Labari: 3480938
Bangaren kasa da kasa, an kafa wasu tantuna na karatun kur'ani a inda ake yada zango ga masu tattakin arbain na Imam Hussain (AS) daga Najaf zuwa Karbala.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa daruruwan masu tafiya ne suke yada zangoa cikin wadannan tantuna domin karatun kur'ani mai tsarki a kowace rana.

Daga jamhuriyar muslucni ta Iran Yusuf Sadighi makarancin kur'ani mai tsarki ya kasance daga cikin masu tilawa, kamar yadda kuma shi ma a nasa bangaren sheikh Muhammad Al-najjar shugaban kula da ayyukan sa kai na hubbaren Imam Hussain (AS) ya gabatar da jawabi da wa'azi ga wadanda suka tarua cikin daya daga tantunan.

Shi am Muhammad Kermani daga jamhuriyar muslucni ta Iran fitaccen makarancin kur'ani mai tsarki ya gabatar da tilawa a daya daga cikin tantunan, bugu da kari kan hakan kuma an gabatar da wakokin yabon manzon Allah tsira da amincin Allah su tababta a gare shi da iyaan gidansa tsarka a wannan babban taro na arbain na Imam Hussain (AS).

Muhammad dahdashti shi ne shugaban kula da wakokin yabon manzo da iyalan gidansa, wanda kuma Muhamad Mizyani ya kasance daga cikin masu taimaka masa domin ganin an saka kumaji na kauna da kishin masu ziyarar da suke yada zangoa tantunan Ghadir kan aikin ziyarar da suka zo.

Abin tuni a nan dais hi ne, tun bayan da aka fara gudanar da irin wadannan ayyuka na ziyarar Imam arbain na Imam Hussain (AS) a cikin shekarun nan, lamarin yana ci gaba da kara bunkasa tare da karbar jama'a daga ciki da wajen kasar.

3545928


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: