IQNA

23:48 - November 15, 2016
Lambar Labari: 3480941
Bangaren kasa da kasa, Hussain Mirzaei Vani jakadan Iran a kasar Venezuela ya bayyana a zantawarsa da radio ALBA CIUDAD cewa wasikar jagora zuwa matasan turai ta yi tasiri.
Kamfanin dillancin labaran kur’[ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto shafin yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslucni cewa, a lokacin da jakadan na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wannan radio CIUDAD a wajen taron baje kolin littafai na duniya a birnin Karakas.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu wasikar jagora zuwa ga matasan kasashen yammacin turai ta yi aggarumin tasiri wajen bayyana ma matasan hakikanin koyarwar addini, har ma da manya da suka hada har da masana daga cikinsu, wadanda suke da karancin sanin muslunci da koyarsa.

Domin kuwa da dama daga ko mafi yawan al’ummomin turai ba su da masaniya kan addinin muslunci, a kan haka abin da suke gani a halin yanzu na ta’addanci da wasu suke yi da sunan muslunci, sai suke huknta muslunci a haka.

Jami’in ya ce akwai matasa da dama da suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da wasikar ta jagora, inda tuni suka dawo daga rakiyar tunaninsu na farko kan muslunci, inda yanzu suka fahimci cewa muslucni addini ne na zaman lafiya da girmama dan adam.

Abin tuni a nan dai shio ne wasikar jagoraan rubuta ne da nufin fadakar da matasan nahiyar turai kan gurguwar fahimtar da suke da ita kan addini, wanda hakan ya sanya wasunsu shiga kungiyoyin kyamar musulmi.

Jami’in na Iran yana halartar wannan baje kolin littafai ne na kasar Venezuela wanda aka yi wa taken FILVEN 2016, kuma za a kammala shi a cikin wannan mako da muke da ciki.

3546170


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: