IQNA

23:52 - November 15, 2016
Lambar Labari: 3480942
Bangaren kasa da kasa, a jiya ne aka ga wata mafi girma kasashen duniya daban-daban da hakan ya hada har da hubbaren Abul Fadhl Abbas (AS) a Karbala.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin telegram na cibiyar musulunci ta Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna cewa, an wata mafi girma ajiya a hubbaren Abul fadhl Abbas (AS).

Bisa ga al’ada duk bayan makonni hudu watan ya matso kusa da kasa, amma wannan ya sha banban matuka, domin girmansa ba irin wanda aka saba gani ba ne, domin kuwa matso kusa da kasa fiye da abin da aka sanbi bisa al’ada.

Wasu masana suna cewa hakan na faruwa ne sau daya a cikin shekaru saba’in, kumaba zai sake faruwa ba sai bayan wasu shekaru saba’in a nan gaba.

A lokacin da aka ga wata ya yi irin wannan shi ne ake kiransa giwan wata, ko kuma (supermoon) a turance.

3546105


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Vienna ، duniya ، wata ، Abbas ، mafi girma
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: