IQNA

20:35 - November 18, 2016
Lambar Labari: 3480951
Bangaren kasa da kasa, kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Iraki ya mayar da hankali wajen kwasar masu ziyarar arbaeen na Imam Hussain (AS) zuwa Karbala.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Brath cewa, jiragen kasa na kasar Iraki ne suke kwasar masu ziyara daga Basara da Bagadaza zuwa birnin karbala mai alfarma, inda a kowace rana sukan yi sawu 54, amma zai kai zuwa 70 a kowace rana.

Jabbar Al-his babban daraktan kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Iraki ya bayyana cewa, sun sanya dukkanin jiragensu da ke zirga-zirga a kasar da su mayar da hankali wajen daukar masu ziyarar arbaeen na Imam Hussain (AS).

Ya kara da cewa wannan abin da suke yi yana a matsayin hidima ga Imam Hussain da iyalan gidan manzon Allah, kuma aiki ne na lada.

Kamfanin jiragen kasa na kasar Iraki yana karbar wasu 'yan kudade daga masu ziyarar, kamar yadda yake bayar da dukkanin abubuwan bukata ga masu tafiya na abinci da sauransu.

3546862


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: